<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>from Southern Harmony, Wesley, Charles (1707-1788)</author>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu Kristi, muna jira
 Alkawalin Allahnmu.
 Annabawa suna shaida
 Kana batun cewarsu
 Za ta yi ciki budurwa
 Ikon Ruhun Allah ne
 Zo da sauri, albarka mu
 Cika duka annabci

[V2]
 2) Baitalahmi, ƙauyen Dauda
 Cikin Yahudiya ne.
 Shi ne wurin haifuwarka
 Yadda Mika ya faɗi.
 Issufu da Maryamu
 Sun yi bulaguro can
 Saboda lissafin ƙasa
 Domin dokar Romawa.

[V3]
 3) Yesu, kana da sunaye
 Kirgarsu, su nawa ne?
 Almasihu da Shafaffe
 Sarkin salama kai ne.
 Begen duniya, Immanuel
 Mashawarci mai kyau ne.
 Kalmar Allah, Hasken haske
 Mai farko da Mai ƙarshe.</lyrics>
<title>Yesu Kristi, Muna Jira LW574</title>
<hymn_number>574</hymn_number>
</song>